12 Satumba 2021 - 13:19
​Iran: Firayi Ministan Iraki Na Ci Gaba Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Tehran

A yau ne Firayi ministan kasar Iraki Mustafa Alkazimi ya fara gudanar da ziyarar aiki a kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, jim kadan bayan isowarsa birnin Tehran, ya samu tarba ta musamamn daga shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi, inda bayan kammala faratin ban girma da aka yi masa a fadar shugaban kasa, bangarorin biyu sun shiga tattaunawa.

Ministocin gwamnatin Iraki 7 ne suke yi wa firayi ministan kasar rakiya acikin tawagarsa a ziyarar tasa a birnin Tehran.

Ana sa ran a yayin wannan ziyara bangarorin Iran da Iraki za su tattauna muhimamn batutuwa da suka shafi alaka da ke tsakaninsu, da kuma kara bunkasata a dukkanin bangarori, musamman a bangaren harkokin tattalin arziki da cinikayya.

Baya ga haka kuma ana sa ran gwamnatocin kasashen biyu za su rattaba hannu kan ayyuka na hadin gwiwa atsakaninsu kan lamurran tsaro, kamar yadda kuma za su rattaba hannu kan yarjeniyoyi da suka shafi makamashi da wutar lantarki.

Ana sa ran firayi ministan Iraki zai gana da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar ta Iran, da suka hada da shugaban majalisar dokoki da kuma shugaban majalisar tsaron kasa.

342/